ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban ya na fadar haka a taron majalisar ministocin kasar da ya saba gabatarwa a ko wace rana a yau Laraba.
Shugaban ya kara da cewa duk duniya ta shaida cewa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar basu kai ga manufar dorasu ba, kuma ba zasu taba kaiwa ba.
Daga karshe shugaban ya bukaci gwamnatin Amurka mai ci ta dawo daga rakiyar wadannan takunkuman, ta kuma ciresu, sannan ta dawo cikin yarjejeniyar JCPOA , a sannane Iran za ta dawo kan alkulanta a yarjejeniyar.
342/